Kwamishinan hukumar INEC a jihar ta Jigawa Alhaji Halliru Aliyu ne ya tabbatar da hakan ga manema labaru a birnin Dutse, fadar gwamnatin jihar.
Aliyu ya ce hakan ya biyo bayan matsalar karancin kayan aikin gudanar zaben da aka ci karo da ita ne. Sai dai ya ce za a gudanar da zaben shugaban kasa, da na 'yan majalissar dattijai a dukkanin kananan hukumomin jihar 27 kamar yadda aka tsara.
Ya ce tuni hukumar ta kammala shiri domin gudanar sauran zabukan kamar yadda doka ta tanada.
Ba a dai sanar da sabuwar ranar gudanar zaben 'yan majalissar wakilan ba.