Hakan a cewar kakakin ma'aikatar tsaron kasar Chris Olukolade, ya biyo bayan hare-hare ta kasa da sama da sojojin suka kaddamar a ranar Juma'a.
Rahotanni daga rundunar tsaron kasar na cewa yanzu haka, garuruwan Abadam dake Arewacin jihar Borno, da Kala Balge, dake yankin tsakiyar jihar ne kadai suka rage a hannun mayakan kungiyar.
Wannan dai ci gaba na zuwa ne 'yan sa'o'i kadan, gabanin fara kada kuri'u a babban zaben kasar na Asabar din nan.
Tun dai a ranar Larabar da ta gabata ne shugaban tarayyar Najeriyar Goodluck Jonathan, ya yi hasashen cewa nan da ranar Juma'a sojojin kasar za su kwato garin na Gwoza.