in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jonathan ya amince da faduwa a babban zabe
2015-04-01 09:50:03 cri

Shugaban Nigeriya Goodluck Jonathan ya amincewa da faduwa a babban zaben da aka gudanar karshen makon nan, lokacin da a ranar Talatan nan ya yi kiran ta wayar salula ga zababben shugaban kasa, kuma 'dan jam'iyyar adawa Muhammadu Buhari.

Muhammadu Buhari wanda ya tabbatar da hakan ga Xinhua cewa, ya samu wayar shugaba Jonathan da misalin karfe 5.15 na maraicen Talatan nan inda yake taya shi murnar lashe babban zabe da aka kammala a kasar.

Wannan kira ta shugaba Jonathan ga abokin hamayyarsa ta yi abin da ba a taba yi ba a tarihin kasar, inda wanda ya fadi zai kira wanda ya lashe zabe nan take ya taya shi murna, in ji tsohon shugaban kasar Janar Abdulsalami Abubakar.

A wani labarin kuma zababben shugaban kasar Muhammadu Buhari ya fitar da sanarwar godiya ga daukacin 'yan Nigeriya da suka zabe shi da jam'iyyar shi a kan jam'iyya mai mulki na PDP.

Kakakin jam'iyyar adawa Malam Shehu Garba ya ce, jam'iyyar ta riga ta hada liyafar murnar lashe zaben a Abuja tare da 'dan takararta Muhammadu Buhari. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China