in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar gwamnatin Jamus ta yi alkawarin yin iyakacin kokarin gano dalilin faduwar jirgin sama
2015-03-27 15:13:38 cri

Shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel ta bayyana a jiya Alhamis cewa, ya zuwa yanzu, ba a gano dalilin da ya haddasa hadarin faduwar jirgin sama na Germanwings ba, kasar Jamus za ta yi iyakacin kokarin bincike kan wannan hadarin.

A wannan rana da yamma, Carsten Spohr, shugaban kamfanin jiragen sama na Lufthansa na kasar Jamus ya yi tsokaci a gun taron manema labaru cewa, wannan hadari ya kasance wani al'amari na musammun, mataimakin matukin jirgin sama ya ci daukacin jarrabawa, yana da kwarewa sosai wajen tuka jirgin sama. Mr. Spohr ya ce, mun yi mamaki sosai a yayin da muke samun labarin da ke nuna cewa mataimakin matukin jirgin ya haddasa wannan hadari da gangan. Amma ba mu iya tabbatar da ainihin dalilin da ya sa ya yi hakan ba. Lallai wannan wani hadari ne da ya wuce zatonmu. Ko wane irin matakin tsaro da kamfanin ya dauka, ba za a iya kawar da irin wannan batun da ya faru ba.

A jiya Alhamis, jami'in hukumar gabatar da kara ta birnin Marseille na kasar Faransa Brice Robin ya ce, yayin faruwar hadarin jirgin saman, mataimakin matuki Andreas Lubitz shi kadai ne ke cikin dakin matuki, kana ya ki bude kofa ga matukin. Shi ya sa, ana ganin cewa, wannan mataimakin matuki na da nufin haddasa wannan hadari, kuma ba a iya tabbatar da cewa wannan wani hari ne na ta'addanci.

A wancan rana kuma, 'yan sanda na kasar Jamus sun kaddamar da bincike kan batun.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China