in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani hadarin jirgin saman kasar Jamus ya hallaka mutane da dama
2015-03-25 14:49:30 cri

Rahotanni na cewa mai yiwuwa ne daukacin mutane 150 dake cikin wani jirgin saman kasar Jamus kirar "Airbus A320" sun rasa rayukan su, bayan da jirgin ya yi hadari a kan hanyar sa ta zuwa birnin Dusseldorf na kasar Jamus, daga birnin Barcelona na kasar Spaniya.

Jirgin fasinjan dai ya fadi ne a yankin tsaunukan French-Alpes dake kudancin kasar Faransa a jiya Talata. Ba a dai kai ga gano dalilin da ya haddasa faruwar hadarin ba, sai dai an riga an gano akwatin nadar bayanan jirgin saman.

Kafofin watsa labarun wurin sun ba da labari cewa, jirgin sama ya fadi ne a tsakiyar wannan rana a kudancin tsaunin na French-Alpes, kuma sassan sa sun warwatsu cikin tsaunin mai tsayin mita 1500 zuwa 2000.

An ce rashin wata hanyar mota ko fili na saukar jirgin sama a wurin da hadarin ya auku, ya haifar da cikas ga aikin ceto.

Shugaban kamfanin jiragen saman Germanwings na kasar Jamus Thomas Winkelmann, ya bayyana cewa jirgin na dauke ne da fasinjoji 144, da kuma ma'aikata 6, da suka hada da jarirai biyu da dalibai 16, kuma cikinsu mutane 67 'yan asalin kasar Jamus ne.

A game da haka, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana matukar juyayi ga rasa rayukan da hadarin jirgin ya haifar, tare da jajantawa iyalai da 'yan uwan wadanda hadarin ya ritsa da su.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China