in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Kenya ya ba da umurni ga manyan jami'ai da ake zargi da cin hanci da su yi murabus
2015-03-27 10:18:06 cri

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyata ya bukaci a ranar Alhamis ga ma'aikatan gwamnati da sunayensu ke cikin wani rahoton kwamitin yaki da cin hanci da rashawa na kasa da su yi murabus nan take.

Da yake gabatar da jawabi kan halin da kasa take ciki a gaban 'yan majalisar dokoki, mista Kenyata ya bayyana cewa, rahoton baya bayan nan kwamitin yaki da cin hanci (EACC) da ya ajiye a gaban 'yan majalisa na dauke da takardun shaidu na zargin cin hanci a matakin koli, da ke shafar dukkan bangarori daban daban da kuma a matakai daban daban na gwamnati.

Na ba da umurni ga dukkan ma'aikatan gwamnatin kasar da na yankuna, da sunayensu ke cikin wannan rahoto, ku kasance sakataren ma'aikata ne, babban sakatare ne ko kuma shugaban zartaswa na wata hukumar kasa ne, to ku yi marabus nan take kafin jiran sakamakon bincike kan zargin da ake yi kan ku, in ji shugaban Kenyata, inda kuma ya kara da cewa, yana fatan cewa, sauran fannonin gwamnati, musammun ma a bangaren hukumomin dokoki da na shari'a su ma za su yi hakan.

Shugaba Kenyata, ya yi kira ga dukkan hukumomin gwamanti da su yi aiki tare da kwamitin EACC yadda ya kamata domin kawar da cin hanci cikin sauri da bala'in da ya janyo.

An yi ta dai bankado harkokin cin hanci a wasu manyan hukumomin gwamnatin kasar da na yankunan kasar a baya bayan nan, wadanda suka hada ma'aikatar makamashi, hukumar zabe mai zaman kanta, da wasu kamfanonin gwamnati da na wasu gwamnatocin jahohin kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China