in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya za ta kafa cibiyar hana yaduwar kananan makamai
2015-03-11 09:39:25 cri

A jiya ne majalisar zartaswar kasar Kenya ta amince da kafa wata cibiyar shiyya kan hana yaduwar kananan makamai a yankin manyan tafkuna na Greta Lakes, kusurwar Afirka da kuma kasashen da ke makwabta da ita.

Wata sanarwa da aka raba wa manema labarai bayan ganawar da shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya jagoranta ta ce, manufar kafa cibiyar ita ce magance matsalar yaduwar kanana da manyan makamai da ke haifar da barazanar tsaro a sassan birane da kauyukan kasar.

Sakataren majalisar zartaswar kasar Kenya mai kula da harkokin tsaron kasa Joseph Nkaissery ya yi gargadin cewa, gwamnatin Kenya ba za ta lamunci duk wani mataki na rashin bin doka ba. Kasar ta Kenya ta kasance a sahun gaba wajen ganin an kawar da yaduwar makamai ne ganin yadda duniya da shiyya-shiyya suka dukufa a wannan fanni.

Matakin kafa cibiyar na zuwa ne bayan da gwamnatin Kenya ta baiwa al'ummomin da ke fada da juna a yankin arewa maso yammacin kasar da ke rika da makamai ba bisa ka'ida ba wa'adin mako guda da su yiwa makaman nasu rijista ko su fuskanci hukunci.

Bayanai na nuna cewa, kafa wannan cibiya ya zo ne a dai-dai lokacin da kasar ke fuskantar matsalar mayakan Al-Shabaab na kasar Somaliya da ke zafafa kai hare-hare a shiyyar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China