in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Namibiya ta nada mace ta farko a kujerar firaminista
2015-03-12 10:08:42 cri

Zababben shugaban kasar Namibiya Hage Geingob ya nada ministar kudin kasar da ta jima kan wannan mukami, madam Saara Kuugongelwa-Amadhila a matsayin firaministar wannan kasa a ranar Labara.

Shugaban ya sanar da wannan nadin a yayin wani taron manema labarai, inda a lokacinsa kuma ya sanar da nada ministan harkokin kula da 'yan mazan jiya na yanzu Nicky Lyambo a matsayin mataimakin shugaban kasa, sabuwar kujerar da aka kafa.

Haka ministan harkokin wajen kasar Netumbo Ndaitwah, an nada shi maitaimakin firaministan kasar.

Wadannan nade nade za su samu amincewa daga majalisar dokokin kasar, in ji shugaban kasar.

Mista Geingob da ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a cikin watan Nuwamban da ya gabata, zai yi rantsuwar kama aiki a ranar 21 ga watan Maris a matsayin shugaban kasar Namibiya na uku. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China