in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an sa ido na AU sun jinjinawa yanayin zabe a Namibiya
2014-12-01 09:58:14 cri

Shugabar tawagar jami'an sa ido ta kungiyar AU a zaben kasar Namibiya jakada Fatuma Ndangiza, ta yabi yadda zaben kasar ya gudana.

Shugabar wakilan tawagar ta AU, ta kuma yi kira ga al'ummar kasar da su ci gaba da bin tafarkin zaman lafiya da lumana, kamar yadda aka gani yayin babban zaben kasar na ranar Juma'a.

A daya hannu kuma jami'an sa idon sun bayyana cewa, ko da yake dokar zabe ba ta kayyade yawan kudin da ya dace a kashe yayin yakin neman zabe ba, duk da haka akwai abin lura game da yadda manyan jam'iyyu ke kashe makudan kudade, irin wadanda ka iya sanya kananan jam'iyyu samun nakasu a zaben.

Kaza lika wakilan na AU sun ja hankalin mahukuntan kasar game da hana masu tabin hankali damar kada kuri'u, matakin da suka ce ya sabawa sashen dokar da ya tanaji baiwa wannan aji na nakasassu, damar shiga harkokin siyasa.

Tawagar jami'an sa idon ta kungiyar AU dai ta kunshi manzannin kasashen Afirka dake kungiyar, da wakilan dandalin PAP, da wakilan hukumomin gudanar da zabuka, tare kuma da kungiyoyin fararen hula daga kasashen Afirka 17. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China