in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban hukumar zabe a Namibiya ya nemi afuwa bisa jinkirin bayyana sakamako
2014-12-01 10:28:42 cri

Babban daraktan hukumar gudanar da zaben kasar Namibiya ECN Farfesa Paul Isaak ya nemi afuwar jama'ar kasar, bisa jinkirin da aka samu na bayyana sakamakon babban zaben kasar da ya gabata a ranar Juma'a.

Daraktan na ECN ya ce, hakan ya faru ne sakamakon jinkirin da aka samu na kammala kada kuri'u a wasu tashoshin zaben kasar.

Ya ce, a baya an tsara kammala zaben 'yan majalissu da na shugaban kasar ne a ranar Juma'a, sai dai matsalar da aka samu, ta sa wasu tashoshin zaben kasancewa a bude har ya zuwa ranar Asabar, lamarin da ya sanya ya zuwa yammacin ranar Lahadi, kaso 30 bisa dari ne kawai na kuri'un aka kai ga kammala kirgawa.

Farfesa Isaak ya kara da cewa, an riga an tattara daukacin alkaluman kuri'un mazabun kasar 121, sai dai tantance su shi ne jan-aikin da ya dakatar da bayyana sakamakon a ranar Lahadi, kamar yadda aka tsara a baya.

Wasu rahotanni dai sun tabbatar da cewa, takardun alkaluman zaben da aka aikewa hukumar ta ECN na cike da kurakurai, wadanda ya zama wajibi a tantance tare da gyara su kafin mai yiwuwa a bayyana sakamakon a Litinin din nan.

Babban zaben kasar ta Namibiya na wannan karo dai shi ne 3, tun bayan samun 'yancin kan kasar daga Afirka ta Kudu a shekarar 1990. Zai kuma ba da damar zaben sabon shugaban kasa, tare da 'yan majalissun dokokin kasar 96. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China