in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Kenya ta rattaba hannu kan dokar yaki da ta'addanci
2014-12-19 10:54:11 cri

Yayan majalisar dokokin kasar Kenya sun rattaba hannu a kan wata doka ta yaki da ta'addanci, duk kuwa da yake cewar ra'ayinsu ya banbanta.

Gwamnatin kasar ta Kenya ta ce, sabuwar dokar za ta taimaka wajen tsaurara matakan tsaro a yankin domin tunkarar barazanar hare-hare na 'yan ta'adda dake kasar ta gabashin Afrika.

Kakakin majalisar dokokin kasar mai shari'a Muturi ya canza jadawalin ajandar taro saboda rikici tsakanin bangaren gwamnati da kuma bangaren 'yan adawa.

Yan majalisar dokoki bangaren gwamnati su ne suka amince da kafa dokar a inda 'yan adawa suka ki amincewa, hakan ya haifar da musayar kalamai masu zafi da kokawa a majalisar.

A yayin rikicin, an hana jama'a da 'yan jarida shiga zauren majalisar, kuma dama a can baya an sha dage zaman majalisar saboda kacamewar fadace-fadace tsakanin bangarorin dake adawa da juna.

Aiwatar da garambawul a kan dokokin tsaro na kasar na shekara ta 2014 duk da yake ya haifar da ka ce na ce, a karshe an amince da shi kuma gyaran fuskar dokokin tsaron na nufin cewar, a yanzu hukumar leken asiri ta kasar tana iya kama duk wani mutumin da ake zargi da aikata laifi, kuma a yanzu shugaban kasa yana iya zaben sipeta janar na kasar, amma kuma tare da amincewar 'yan majalisar dokokin kasar. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China