in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin Afrika sun yi alkawarin magance talauci da rashin daidaito
2015-02-26 10:41:50 cri

Ministocin Afrika za su inganta zuba jari a ayyukan walwalan jama'a da suka hada da ilimi da kiwon lafiya domin magance talauci da samar da daidaito.

Ministocin tare da sauran masana da masu fafutuka dake halartar babban taron walwala a birnin Nairobi na kasar Kenya sun lura da cewar, tsananin talauci, rashin daidaito da wariya ke dakushe ci gaban nahiyar.

Mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto ne ya bude taron ministocin da za'a tattauna shirin da za'a kirkiro da kuma hanyar samun kudin da za ta azazzala ci gaban walwala da tattalin arzikin nahiyar wanda ofishin UNESCO ta MDD ta shirya.

Mr. Ruto ya jaddada cewa, yanayin sauyin gwamnatoci da kula da albarkatun kasa ya zama abin sauri domin farfado da nahiyar. Ilimi ya zama jigo mai muhimmanci ga inganta walwala al'umma wanda ba abin da za'a yi sakaci da shi ba ne. Ya kara da cewa, da niyya kasar ta fadada ilimin makarantun sakandarenta saboda tana son ko wane yaro ya samu damar ilimi na ainihi.

Ya lura da cewar, gaba daya kashi 31 a cikin 100 na kasafin kudin kasar ta Kenya, an karkata shi ne zuwa ga ilimi, kuma gwamnati ta kara kudin tallafi na karatu a wannan shekara daga dala miliyan 308 zuwa dala miliyan 440 wanda yake wakiltar karin kashi 35 a cikin 100. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China