in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kafofin watsa labarai na Afrika na taro a N'Djamena
2015-02-03 12:47:27 cri

Zaman taro karo na shida na dandalin manyan editocin Afrika, ya bude a ranar Litinin a birnin N'Djamena, hedkwatar kasar Chadi bisa taken "kafofin watsa labarai da tashe tashen hankali a Afrika: annoba da rashin tsaro." in ji wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

A tsawon kwanaki uku, shugabannin kafofin watsa labarai na Afrika za su mai da hankali kan matsayin jarida a gaban matsalolin tsaro daban daban, da kuma yawan annobar da ake fuskanta a nahiyar Afrika. Matsalar rashin tsaro da 'yan ta'adda ke janyo bai bar kowa ba, kuma yaki da kungiyar Boko Haram dake aikata manyan laifuffuka ba nauyin gwmantoci kawai ba, in ji faraministan kasar Chadi, Kalzeube Payini Deubet, a cikin jawabinsa na bude taron a birnin N'Djamena.

Mista Payini Deubet ya bukaci kafofin watsa labarai na Afrika da su ci gaba da ba da kokari, bisa tunani mai kyau wajen yaki da rashin tsaro, da kuma yin nazari sosai kan majiyoyi da dalilai da kuma bayyana su ga jama'a yadda ya kamata.

Dandalin editocin Afrika, wata kungiyar Afrika ce dake kunshe shugabannin kafofin watsa labarai na gwamnati da masu zaman kansu da kuma malaman jami'o'i da suka kware a fannin aikin jarida. Taron N'Djamena na gudana ne, bayan wanda aka yi a birnin Kigali na kasar Rwanda a shekarar 2012. An kafa kungiyar shugabannin kafofin watsa labarai na Afrika yau da kusan shekaru goma, haka kuma kungiyar tana da rassanta a yankunan Afrika daban daban, kuma babbar cibiyarta na birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China