in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ECCAS ta yi kira ga kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya da ta kafa kungiyar shugabancin rikon kwarya
2013-04-04 17:04:03 cri
Kungiyar cigaban tattalin arziki na kasashen yankunan tsakiyar Afrika wato ECCAS ta nuna a ran 3 ga wata cewa, ba ta amince da kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya da ta nada shugaba da kanta ba, don haka ta yi kira ga kasar da ta kafa wata kungiyar shugabancin rikon kwarya domin gudanar da ayyukan kasar.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a lokacin wani taron koli na musamman da ta kira a wannan rana a N'Djamena babban birnin kasar Chadi inda Shugaban kasar Idriss Deby wanda yanzu ke rike da shugabancinta ya ce, kungiyar na ba da shawara ga bangarori daban-daban na kasar Afrika ta tsakiya da su hada kai domin kafa wata kungiyar shugabanci domin gudanar da ayyukan kasar yayin lokacin wucin gadi wanda bai wuce watanni 18 ba, tare da nada wani shugaban kasa na rikon kwarya. A cewar shi ya kamata, kasar ta kafa wata hukumar da za ta gudanar da ayyukan majalisar dokoki domin tsai da tsarin mulki a lokacin wucin gadi.

Shugabannin kasashe daban-daban ciki hadda Kongo Brazzaville, Equatorial Guinea, Gabon, Afrika ta kudu, Benin da wakilin kasar Kongo Kinshasa da kuma firaministan gwamnatin hadin gwiwa ta Afrika ta tsakiya da tawagarsa suka halarci wannan taro. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China