in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya yi kira da a goyi bayan shirin samar da zaman lafiya a Darfur
2014-04-25 14:24:00 cri

Shugaban gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, ya yi kiran goyon baya na kasashen duniya, wajen ingiza kungiyoyi masu yaki da juna a Sudan ta Kudu samar da zaman lafiya mai dorewa, musamman a wannan lokacin da ake samun karuwar hare-haren 'yan tawaye da kuma arangama da juna, saboda rikicin siyasa da matsalolin rasa muhallai, da suka jefa yankin cikin hali na rashin sanin inda aka dosa.

Karamin sakatare gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya Herve Ladsous, wanda ke jawabi ga kwamitin tsaro na MDD a kan halin da ake ciki a Sudan ta Kudu, da kuma batun ayyukan kiyaye zaman lafiya na rundunar hadin gwiwa ta Afrika da MDD watau UNAMID ya ce, an samu hudowar sabbin kalubale a rikicin da ake yi, tun farkon shekara da ake ciki ta 2014, kuma wannan sabon kalubale, ya yi tasiri a kan farar hula na kasar ta Sudan ta Kudu.

Ladsous ya jaddada mahimmanci dake akwai na ingiza kungiyoyin masu adawa da su daidaita da juna.

A halin da ake ciki, Darfur na fuskantar barkewar sabbin rikice-rikice, bayan da rikicin ya dan sarara, musamman a yayin da wadanda suka rasa muhallansu ke ta ficewa, karin samun rashin jituwa a tsakanin masu kawance da gwamnatin Sudan ya haddasa kara tada fitina a Darfur. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China