Shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou ya fara wani rangadin aiki na kwanaki uku a kasar Aljeriya tun daga ranar Lahadi.
Bayan saukarsa daga jirgin sama, shugaban kasar Nijar ya samu tarbo daga shugaban zauren dattawan kasar Aljeriya, Abdelkader Bensalah.
A ranar farko ta ziyararsa, shugaban Nijar ya je babban ginin kamfanin kasa na manyan motoci (SNVI) na Rouiba dake shiyyar gabashin birnin Alger.
Haka kuma, a yayin wannan ziyara, Mahamadou Issoufou zai tattauna tare da takwaransa na kasar Aljeriya Abdelaziz Bouteflika domin kara dankon zumunci da dangantaka dake tsakanin kasashen biyu dake makwabtaka da juna, in ji fadar shugaban kasar Aljeriya a cikin wata sanarwa.
Baya ga yaukaka huldar dangantaka, bangarorin biyu za su kuma mai da hankali kan batutuwan kasa da kasa da na shiyya shiyya dake janyo hankalinsu, musammun ma batun warware rikicin arewacin kasar Mali da na Libiya, da kuma batun yaki da ta'addanci da manyan laifuffukan kasa da kasa a yankin Sahel. (Maman Ada)