Gwamnatin kasar Zambia ta ce, ba za ta lamunta ba da masu yada jita-jita musamman a wannan lokaci da ake gab da gudanar da zaben shugaban kasa na kasar a mako mai zuwa.
Babban kakakin gwamnatin kasar ta Zambia, Joseph Katema ya ce, gwamnatin kasar ta damu ainun da halayyar wadansu jam'iyyun siyasa na kasar, musamman jam'iyyar adawa ta UPND, wace ke ci gaba da gabatar da kalamai da ka iya haddasa fitina da tashin hankali a kasar.
A makon da ya gabata ne shugaban jam'iyyar ta UPND Hakainde Hichilema ya gabatar da sanarwa cewar, ya riga ya lashe zaben shugaban kasar, kuma a ranar Asabar sai mabiyan shi suka dakatar da wadansu manyan motoci na hukumar zabe ta kasar, saboda zaton da suke yi na cewa, manyan motocin suna makare da takardun zabe wadanda suke zaton an shirya domin gwamnati ta goyi bayan dan takarar gwamnatin kasar, to amma da 'yan sanda suka duba motocin, babu kome a ciki, in ban da kujeru da tebura da sauran kayayyaki mallakin hukumar zabe ta kasar Zambia.
Kakakin gwamnatin ya yi kira a kan jam'iyyar ta UPND da ta dakatar da jita-jitar da take yadawa, kuma ya yi gargadi cewar, za ta tabbatar da daukar mataki na doka a kan wadanda ke da alhakin yada jita-jitar.
Kasar Zambia za ta gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 20 ga watan Janairun da muke ciki, bayan rasuwar shugaban kasar ta Michael Sata a watan Oktobar shekarar bara. (Suwaiba)