in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawa suna kokarin taimaka wa Uganda a fannin aikin gona
2015-01-05 17:03:47 cri

Sakamakon karuwar cudanya a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a fannonin tattalin arziki da cinikayya, al'adu, aikin gona da dai sauransu a shekarun baya, yanzu Sinawa dake kokarin karfafa irin cudanya a nahiyar Afirka na ta karuwa. A kasar Uganda dake gabashin Afirka, akwai wasu kwararru da ma'aikata a fannin aikin gona suke kokarin domin kara sada zumunta a tsakanin kasashen biyu.

Kasar Uganda na da yanayi mai kyau, kuma kasa ce mai albarkatu, hakan ya sa tsohon firaministan kasar Burtaniya Churchill ya kiranta "lu'u lu'u na Afirka", yanayin hallitu da kasar ke ciki ya dace wajen bunkasa aikin gona sosai. Bisa shirin musamman na samar da isassun hatsi da kungiyar abinci da aikin gona ta MDD wato FAO ta kaddamar, tare da taimakon gwamnatin kasar Sin da kuma gwamnatin Uganda, sun soma gudanar da ayyukan hadin kan sha'anin noma tsakanin kasashe masu tasowa da suka shafi Sin da Uganda daga karshen shekarar 2012, ya zuwa yanzu dai an kammala karon farko na wannan aiki yadda ya kamata. Shugaban kungiyar kula da aikin mista Wu Zhiping ya bayyana cewa, muhimmin abu na wannan aiki shi ne aiwatar da ayyukan habaka fasahohin aikin gona a wurin. Wu ya ce,

"a karkashin jagorancin kungiyar FAO ne mun tura kwararru da ma'aikata a fannin aikin gona zuwa kasar Uganda, don yin cudanya da hadin kai kan fasahohi tare da kwararru da ma'aikata na ma'aikatar sha'anin noma ta kasar. Muna dora muhimmanci kan gabatar musu wasu sabbin nau'o'in kayayyakin noma da sabbin fasahohi masu amfani, don daga matsayinsu na sha'anin noma, da samun hatsi mai yawa, kana da kara kudin shiga na manoma. "

A cikin shekaru biyu da suka wuce, wadannan kwararru da ma'aikata 31 da suka fito daga kasar Sin sun hada kai sosai tare da ma'aikata na wurin da manoma, yayin da suke kara sada zumunta a tsakaninsu, a sa'i daya kuma sun samu sakamako mai kyau. Mista Wu ya bayyana cewa,

"a karkashin goyon baya daga wajen shugaban gwamnatin gundumar Budaka ta kasar Uganda, kwararrunmu a fannonin kiwon hallitun ruwa, da hatsi da kuma samar da harawa sun gyara harawar kifi da kansu, da neman hanyar kiwon kifi a tafki, wannan tsarin da ake bi ya taimakawa iyalan manoma samun sakamako mai kyau. Saboda haka, kafin mu tashi daga wurin, shugaban gwamnatin gundumar ya ce, kwararru da ma'aikata na kasar Sin sun kawo musu wani babban sauyi daga tushe."

Bayan haka kuma, kwararru da ma'aikata na kasar Sin su ma sun burge shehun malami James Tumwine, jami'in dake aikin hadin gwiwa kan sha'anin noma na bangaren Uganda, inda ya bayyana cewa,

"Mutane ne masu kirki, sun nuna himma da kwazo kan aiki, kuma sun nuna mana dukkan fasahohin da suke da kwarewa kansu. Suna son aiki tare da mu, da kuma tattauna fasahohi a fannin aikin gona. Mun yi farin ciki da gudanar da aiki tare da su, don ciyar da aikin gona gaba."

A watan Agusta na shekarar 2014, a yayin da yake ganawa tare da tawagar sha'anin noma ta lardin Sichuan na kasar Sin, mataimakin shugaban kasar Uganda Edward Ssekandi ya bayyana cewa, kasarsa na fatan kasar Sin za ta kara zuba jari kan sha'anin noma a kasashen Afirka. Shugaban kungiyar hadin kan aikin gona ta kasar Sin Wu Zhiping ya gabatar da cewa, ban da hada kai da ma'aikatar sha'anin noma, da hukumomin nazari, da gwamnatocin kananan hukumomi, da kuma gandunan noma masu zaman kansu na kasar Uganda, don habaka ayyukan ba da misali kan fasahohi a kasar, sun kuma sa himma wajen neman hanyar hadin kai tsakanin kasashen biyu ta fuskar zuba jari kan sha'anin noma. Wu ya ce,

"Bisa kokarin da muka yi a shekarar da ta wuce, akwai kamfanoni guda 7 na lardin Sichuan da suka tabbatar da zuba jari kan aikin gona a kasar Uganda. Bisa shirin da suka yi, a cikin farkon shekara za su zuba jari na kudin Sin RMB miliyan 50 zuwa miliyan 100, a cikin shekaru biyar masu zuwa kuma za a kammala zuba kudi RMB miliyan 300 zuwa 500, ta yadda za a iya inganta bunkasuwar tattalin arziki da kauyukan kasar ta hanyar aikin gona. Yanzu ayyukan da wadannan kamfanoni suka yi da fatan da suka bayyana game da zuba jari sun jawo hankalin gwamnatin kasar Uganda sosai."

Bisa labarin da muka samu, domin biyan bukatun ma'aikatar sha'anin noma ta kasar Uganda, bayan da aka samu amincewa daga wajen kungiyar FAO da ma'aikatar sha'anin noma ta kasar Sin, za a soma aiki karo na biyu na ayyukan hadin kai tsakanin kasashe masu tasowa da suka shafi Sin da Uganda a watan Maris na shekarar 2015. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China