Ayyukan dandalin kasar Tunisia kan zuba jari (TIF 2012) sun soma tun ranar Alhamis da yamma bisa taken " sabuwar kasar Tunisia, kalubalan da za'a fuskanta da kuma hanyoyin moriya da za'a samar" bisa babban makasudin kusanto manyan 'yan kasuwa da manufar kasar Tunisia a matsayin wata makomar kasuwa mai tattare da alfanu da kariya.
Dandalin TIF 2012 na wannan karo ya samu halartar mutane 1.580 da suka fito daga kasashe 35.
Jadawalin wannan zaman taro na kwanaki biyu zai hada da taruruka aiki hudu, gabatar da jawabai 25 da kuma bada kyaututtuka goma ga kamfanonin kasashen waje dake kasar Tunisiya.
Ministan zuba jari da hulda da kasashen waje na kasar Tunisiya, Riadh Bettaieb da ya shugabanci bikin bude dandalin ya nuna cewa, alkaluma na tattalin arzikin kasar Tunisiya sun bayyana kyautatuwar harkoki a wannan fanni a cikin watanni biyar na farkon shekarar 2012 tare da samun bunkasuwar zuba jarin waje kai tsaye (IDE) da kashi 12.5 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar 2010 da kuma na shekarar 2011 dake kashi 41 cikin 100. (Maman Ada)