Taron aiki kan zirga-zirgar fasinjoji da jiragen sama ya gudana a duk kasa na shekara ta 2014 ya sanar da cewa, ana kyautata zaton cewa, yawan fansinjojin da aka yi jigilarsu da jiragen sama a shekarar 2013 ya kai miliyan 354, wanda ya karu da kashi 11 bisa dari, wanda ya kai kashi 1 cikin tara na dukkan fasinjojin da aka yi jigila a duk duniya.
A gun taron, an yi hasashen cewa, sha'anin zirga-zirgar jiragen sama na fasinja zai dauki kaya da yawansu zai kai ton-kilomita biliyan 748, yawan fasinjoji zai kai miliyan 390, yawan kayayyakin zai kai ton miiyan 587, wadanda za su karu da kashi 11.1, da 10.5 da 5.3 bisa dari bi da bi.(Danladi)