Jiragen sama suna tafiya a yankin kamar yadda ya kamata, in jin kakakin harkokin wajen kasar Sin
A gun taron manema labaru da aka shirya a ran 28 ga wata a birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mista Qin Gang ya bayyana cewa, bayan da aka fitar da sanarwar shata yankin tsaro a sararin samaniya a tekun gabas na kasar Sin, jiragen sama suna tafiya a yankin kamar yadda ya kamata, musamman ma jiragen sama na jama'a ba tare da an kawo musu wani tangarda ba.(Danladi)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku