Karamin ministan ma'aikatar kudi a Nigeria Yerima Ngama ya ce, yawan hannayen jarin da Nigeria ke da shi a bankin duniya sun karu da 119, matsayin da ya sanya jimillar hannayen jarin kasar kai wa sama da 1,000, a cewar ministan, hakan ya biyo bayan wani sauyin da bankin ya aiwatar don gane da korafin da ake yi, na cewa, bankin na nunawa kasashen dake nahiyar Afirka banbanci. Ngama wanda ya bayyana wa manema labaru wannan ci gaba ranar Laraba 9 ga wata, bayan kammalar taron majalisar zartaswar kasar, ya kara da cewa, wannan mataki tamkar nuna amincewa ne da irin bukasar da tattalin arzikin kasar ke samu a halin yanzu, zai kuma kara daukaka matsayinta a tsakanin kasashe dake da jari a bankin. Bugu da kari, Ngama ya ce, wannan nasara da Nigeria ta samu ya nuna tagomashin da shirye-shiryen habaka tattalin arzikin gwamnatin kasar mai ci ke samu, wanda a cewarsa, hakan na iya dada habaka harkokin zuba jarin kasashen waje a wannan shekara ta 2013.
Bisa kididdiga kasashe 16 ne cikin 118 ke sahun gaba a yawan jarin babban bankin na duniya, inda a cikinsu, kasashen Afirka ta Kudu da Nigeria ne kadai ke daga nahiyar Afirka.(Saminu)