in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta yi tir da tsawaita takunkumin da Amurka ta kakaba mata
2013-11-01 13:13:53 cri

Mahukuntan kasar Sudan sun yi Allah wadai da tsawaita wa'adin takunkumin da Amurka ta kakabawa kasar zuwa shekara mai zuwa.

Cikin wata sanarwa da ma'aikatar lura da harkokin wajen kasar ta Sudan ta fitar, kan wannan batu na tsawaita wa'adin takunkumin, wanda zai fara aiki tun daga 3 ga watan nan na Nuwamba, ma'aikatar ta nuna takaicin matakin da Amurkan ta dauka, tana mai watsi da dalilan da aka bayyana domin halasta hakan.

Sanarwar ta ce, tun cikin shekarar 1977, Amurkan ke fidda dalilai mabanbanta, domin tabbatar da bukatar dorewar takunkumin da aka dorawa kasar ta Sudan, tare da daukar matakan kassara tattalin arzikinta bisa dalilai na siyasa. Daukar irin wadannan matakai, a cewar waccan hukuma kan kasashen Larabawa da na musulmi, abu ne da sam bai dace ba.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai shugaba Barack Obama na Amurka, ya mika sanarwar tsawaita wa'adin takunkumin na Sudan, gaban zauren majalissar dokoki, yana mai bayyana rashin gamsuwa da manufofi, da tsare-tsaren gudanar da mulkin Sudan din, yana mai cewa, manufofin kasar ba su dace da kudurorin da kasarsa ta sanya a gaba ba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China