in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan masu matsakaicin karfi a Afirka na karuwa
2014-08-27 16:11:45 cri

Bankin SBSA na kasar Afirka ta kudu, wanda ya kasance banki mafi girma a nahiyar Afirka ya fidda wani rahoto a 'yan kwanakin baya, wanda ke fashin baki game da matsayin tattalin arzikin matsakaita daga al'ummun nahiyar, ko "Understanding Africa's middle class"a turance.

Rahotan ya bayyana cewa, masu matsakaicin karfi a nahiyar 'yan kadan ne, amma a baya bayan nan adadin su na ci gaba da karuwa. Rahoton na nuna cewa, a yanayin da ake ciki na samun saurin bunkasuwar tattalin arziki a nahiyar Afirka a 'yan shekarun nan, yawan masu matsakaicin karfi a nahiyar na kara jawo hankulan kasashen duniya.

Bisa bayanin a aka yi cikin wannan rahoto, an yi nazari kan yanayin da iyalan 'yan Afirka suke ciki game da samun kudin shiga bisa ma'aunin kudaden da suke kashewa, inda aka kasa kudaden shigar al'ummar nahiyar Afirka zuwa gida 4. Akwai kashin masu karamin karfi, wadanda ke kashe kasa da dala 15 a kowace rana, da kashin masu matsakaicin karfi dake kasha daga dala 15 zuwa 115 a ko wace rana, sai wadanda ke kashe daga dala 15 zuwa 23 dake ajin masu rauni na matsakaita, da kuma wadanda ke kashe daga 23 zuwa 115 dake ajin matsakaita, ya yin da wadanda ke kashe sama da dala 115 ke ajin matsakaitan masu karfi.

Bayan da aka yi nazari kan iyalai kimanin miliyan 110 daga kasashen Afirka 11, ciki har da wasu al'ummun Angola, da Habasha, da Ghana, da Kenya, da Mozambique, da Najeriya, da Sudan ta Kudu, da Sudan, da Tanzania, da Uganda da kuma Zambia, manazartan sun gano cewa, iyalai miliyan 15 ne kawai ke ajin masu matsakaicin karfi, saura kashi 86 cikin dari masu karamin karfi ne.

Sai dai kafin hakan, wani nazarin na daban da bankin raya Afirka ya yi, ya shigar da mutanen Afirka miliyan 350 a matsayin masu matsakaicin karfi, wadanda yawansu ya kai kashi 1 cikin kashi 3 bisa daukacin al'ummun nahiyar ta Afirka.

Dalilin da ya haddasa wannan gibi shi ne, bankin raya Afirka ya yi nazari ne bisa kudin shiga da mutane ke samu, wato ya mai da mutanen da yawan kudin shiga da suke samu a ko wace rana ya kai daga dala 4 zuwa 20 a matsayin masu matsakaicin karfi.

Ko da yake akwai bambanci game da alkaluman da aka samu sakamakon bambancin hanyoyin da aka bi, duk da hakan ana iya tabbatar da cewa, yawan masu matsakaicin karfi a nahiyar Afirka na karuwa.

Babban daraktan zartaswa na bankin raya Afirka Mista Paul Mwai ya nuna cewa, ko da yake akwai yiwuwar kasancewar gibi tsakanin yawan masu matsakaicin karfi na gaskiya, da wanda alkaluman bincike suka nuna, a hannu guda yawansu na saurin karuwa, ta la'akari da karuwar kudin da matasan nahiyar ke kashewa, musamman ma a fannonin mallakar gidaje, da sayen tuffafi da kuma motoci.

An kuma tabbatar da hakan ne a cikin wasu rahotanni. Wani rahoton da tuni dai bankin raya Afirka ya bayar ya nuna cewa, tun daga shekarar 1980, yawan karuwar masu matsakaicin karfi a nahiyar Afirka ya kai 3.1 cikin 100, wanda ya wuce yawan karuwar mutanen nahiyar baki daya na kashi 2.6 cikin 100.

Ban da wannan kuma, a wani sabon nazari da bankin SBSA ya yi ya nuna cewa, a shekarar 2000 akwai iyalai masu matsakaicin karfi miliyan 4.6 kacal a kasashe 11 da muka ambata a baya, amma ya zuwa yanzu yawansu ya kai miliyan 15. Rahoton ya kuma bayyana cewa, a Najeriya wadda ke kan gaba wajen samun saurin bunkasuwar tattalin arziki a nahiyar Afirka, akwai iyalai masu matsakaicin karfi miliyan 4.1 a yanzu haka, adadin da ya ninka sau 7 bisa na shekarar 2000. A kasar Kenya ma, yawan iyalai masu matsakaicin karfi ya ninka sau biyu a cikin shekaru 15 da suka wuce, haka kuma bisa shirin da kasar ta tsara, ya zuwa shekarar 2030, kasar za ta zama cikin masu matsakacin karfi a duniya, lokacin da yawan iyalai masu matsakaicin karfi zai kai miliyan 1.1, wato yawansu zai kai kashi 8 cikin 100 bisa na dukkan kasar baki daya.

Kwararre a fannonin siyasa da tattalin arziki na bankin SBSA Mista Simon Freemantle ya bayyana cewa, saurin karuwar masu matsakaicin karfi a kasashen Afrika ya nuna cewa, an samu sauyin tsari a nahiyar. Amma, a sa'i daya kuma ya yi gargadin cewa, a yanzu haka yawancin iyalai a nahiyar masu karamin karfi ne, kuma yawancinsu na fama da talauci, hakan dai ya kasance wani babban kalubale da nahiyar ke fuskanta, wanda kuma ke bukatar a nuna hakikanin kwazo wajen tinkarar sa. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China