in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Magatakardan MDD ya bukaci a zuba jari mai inganci a Afrika
2014-07-18 10:37:46 cri

Magatakardan MDD Ban ki-moon a ranar Alhamis 17 ga wata ya yi kira da a kara yawan jarin da ake zubawa a nahiyar Afrika domin a samu cigaban nahiyar mai karko yadda ake bukata.

Mr. Ban da yake bayani a babban zauren mahawarar majalissar dangane da inganta zuba jari a Afrika, ya ce, a cikin 'yan shekarun nan, hauhawar tattalin arzikin nahiyar Afrika ta fi na wassu yankuna da dama a duniya.

Masanan tattalin arzikin majalissar sun yi kiyasin cewa, a shekara mai kamawa ta 2015, cigaban tattalin arzikin nahiyar gaba daya zai haura kashi 5 a cikin 100, musamman a bangaren bukatun cikin gida da farashin kayayyakin yau da kullum.

Sai dai wannan cigaba mai inganci bai kamata ya sa a saki jiki ba, in ji Mr. Ban, yana mai bayanin cewa, har yanzu akwai manyan abubuwan dake kawo cikas ga cigaban tattalin arziki da walwalan jama'a.

Magatakardan majalissar daga nan ya yi nuni da cewa, kamar yadda ake kokarin daidaita shirin cigaba na shekara mai kamawa ta 2015, wanda zai isar da rayuwa mai inganci ga kowane mahaluki a bayyane, yake cewa, Afrika tana bukatar a zuba mata jari mai muhimmanci. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China