Yayin da ya ke zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Sam Mensah, kwararre kan harkokin tattalin arziki, kana mamba a kwamitin hannayen jarin hukumomi(CBC) a ma'aikatar kudi da tsare-tsaren tattalin arziki(MOFEP), ya bayyana cewa, manufar wannan shiri, ita ce a bunkasa kamfanonin kasar, ta yadda su ma za su rika shiga kasuwanni suna bayar da jari.
A kasar ta Ghana, bankin HFC ne kadai ya ke da hurumin bayar da kudade a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta kasar, wanda kuma babu wata riba mai yawa.
Mensah ya shaidawa dandalin kasuwar hada-hadar hannayen jari ta kasar(GSE) cewa, suna son su bunkasa a kalla kamfanoni 6 cikin dan kankanin lokaci ta yadda da za su rika taka rawa a wannan harka nan zuwa a kalla shekaru 2, inda aka lissafa sunayen wasu kasuwanni da kuma dillalai da za su fara amfana da shirin.
Ya ce, idan aka samar da wannan kasuwa, kamfanoni za su samu rabi da dama maimakon su dogara kan bankuna, inda ake tsauwala masu kudin ruwan da za su biya cikin karamin wa'adi na bashin da aka ba su.
Mensah ya kuma jaddada cewa, a daya bangaren kuma, kasuwar hada-hadar kudi ita ma za ta taimakawa kamfanonin wajen samun rance da za su biya cikin dogon wa'adi da kudin kasar na Cedi, ta yadda ba za su fuskanci matsalar canjin kudi ba. (Ibrahim)