in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin cika shekara daya da kafa cibiyar al'adun kasar Sin a Abuja
2014-09-19 13:50:35 cri

Kamar yadda jakadan kasar Sin dake Najeriya Mista Gu Xiaojie ya ce a yayin wannan bikin, aka kafa cibiyar al'adun kasar Sin a Abuja ne tare da sa idon ministan al'adun Najeriya Mistsa Edem Duke gami da shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato Mista Zhang Dejiang a shekarar da ta gabata, shi ya sa wannan cibiya ta kasance tamkar wata jaririya ga dukkan kasashen biyu. Tun lokacin kafuwarta ya zuwa yanzu, cibiyar al'adun kasar Sin tana taka rawar a-zo-a-gani wajen yada nagartattun al'adun kasar Sin a Najeriya, da kuma taimakawa mu'amalar al'adu da ilimi tsakanin al'ummomin kasashen biyu. Jakada Gu Xiaojie yana fatan cibiyar zata cigaba da kara bada gudummawa wajen karfafa zumunci tsakanin Sin da Najeriya, musamman ma a fannin al'adu.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China