in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta samu ci gaba a fannin masana'antun hada motoci
2014-08-01 17:17:04 cri

Nijeriya ta fitar da motar ta na farko da ta hada a watan Yuni a jihar Lagos dake kudancin kasar bisa hadin gwiwar da kamfanin Stallion na kasar ya yi tare da kamfanin Nissan, kera, abin da ya kasance ci gaban da ta samu a fannin masa'antun hada motoci karkashin manufar raya masana'antun kera motoci da gwamnatin ke aiwatarwa. Hakan kuma, kamfanonin duniya da dama su ma suna gabatar da shirinsu na kafa masana'antunsu a Najeriya don fara harkokinsu a Najeriya da sauran kasashe dake kewayenta.

Wannan mota da Najeriya ta kera, kamfanin Nissan da kamfanin Stallion ne suka hada hannu wajen kera ta. A sa'i daya kuma, kamfanin Innoson na kasar Najeriya yana kokarin kera mota ta hanyar hada sassan kayayyakin mota. A nasu bangare suma, kamfanonin motoci a duniya kamar su Kia na Korea ta kudu, kamfanin Tata na kasar Indiya da dai sauransu, sun gabatar da shirin su na kafa masana'antun samar da sassan kayayyakin mota a Najeriya. An yi kiyasin cewa, ya zuwa watan Yuni na wannan shekarar, kamfanoni 12 na kasashen waje sun bayyana burinsu na kafa masana'antunsu a Najeriya. Abin da ya nuna cewa, hakar Nijeriya ta fara cimma ruwa a shirinta na raya sha'anin mota.

A hakkika dai, wannan ba karo na farko ke nan da Najeriya ta yi shirin raya masana'antun kera motoci. Tun a shekarun 1970, Najeriya ta yi kokarin hada kai da kamfanoni kamar su Peugeot Volkswagen, Mercedes da General Motors tare da kara buga haraji kan shigo da mota. Amma, ba a samu ci gaba mai dorewa ba bisa wasu dalilai. Har ya zuwa shekarun 1990, domin neman taimako daga asusun ba da lamuni na duniya IMF da bankin duniya, ba yadda ta yi sai kasar ta karkatar manufofinta da suka shafi cinikayya, tare da rage harajin da ta buga kan mota da aka shigo.

Bisa sabuwar manufar da ta dauka, Najeriya ta daga harajin da ta buga kan kananan bas-bas da ta shigo daga ketare daga kashi 20 zuwa 70 bisa dari, harajin da za a ragu da shi zuwa kashi 55 bisa dari har zuwa shekakar 2019. Kwatanta da haka, an cire haraji kan sassan kayayyakin mota da aka shigo da su daga ketare domin hada su a kasar, sauran kayayyaki da za a shigo da su kuma ana samar da gatanci a fannin faraji. Ban da haka kuma, Najeriya ta ware kudade domin samarwa masu sayen mota rancen kudi tare da nuna goyon baya ga masana'antun kera motoci da sauran kamfanoni dake da nasaba da wannan sha'ani da su kafa farfajiyar masana'antunsu. Ta wannan sabon tsari, gwamnatin kasar na nufin samar da guraben aikin yi 70,000, da kuma samar da guraben aikin yi 210,000 a kananan da matsaikacin kamfanoni ta hanyar habaka sha'anin nan.

Kasashen Afrika ba su rasa samun nasarori a fannin raya masana'antun kera motoci, alal misali, bayan da Afrika ta kudu ta gabatar da manufar sa kaimi ga shigo da sassan kayayyakin mota a shekarar 1995, yawan motocin da ta fitar zuwa kasashen waje ya karu sosai, kudin da ta samu kuma ya yi ta karuwa har zuwa dala biliyan 10.6 a shekarar 2012 daga dala miliyan 490 a baya baya. Hakan ya sa, masana'antun kera motoci sun zama wani babban ginshiki ga sha'anin kere-kere na kasar, inda yawan motocin da ta fitar ya kai kashi 80 bisa dari na dukkan Afrika.

Amma wasu manazarta sun nuna cewa, idan Najeriya ta dauki darasin Afrika ta kudu da nufin raya sha'anin kere-kere ta hanyar bunkasa sha'anin mota, za ta fuskanci kalubaloli da dama. Alal misali, saboda bukatun jama'a a fannin motoci a nahiyar Afrika yana danganta sosai da farashinsu, don haka kayyade kudin da za a zuba da tsai da farashin mota ya zama muhimmin mataki wajen kara karfin yin takara, abin dake da nasaba sosai wajen samun nasara a fannin sha'anin mota. Ban da haka kuma, kasar na fama da yin safarar motoci, saboda sukurkucewar hukumomi masu kula da harkokin kan iyakar kasa da batun cin hanci da karbar rashawa, dimbin motoci na hannu biyu sun kutsa kai cikin Najeriya a ko wace shekara, abin da ya kawo illa ga masana'antun kera motoci a kasar. Wadannan matsaloli tilas gwamnatin da kamfanoni da abin ya shafa su dauki matakan da suka dace domin magance su. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China