Masana sun yi kira a ranar Litinin ga manoman dake gabashin nahiyar Afrika da su rika amfani da hanyoyin da ba na sinadarai ba wajen yaki da kazuwar tumatin Tuta Absoluta dake yaduwa cikin sauri.
Da suke magana a yayin taron shiyya kan cutar tumatir a birnin Nairobi, kwararru da masu bincike a wannan fanni sun bayyana cewa, wannan cuta ta janyo ja da bayan noman tumatir a duniya baki daya tun bakin shekarar 2009, lamarin dake zama babbar bazarana ga yaduwar wannan cuta.
Ana iyar daidaita cuta cikin karko ta hanya guda wato dabarun yaki kwari (LAI) ta hanyar amfani da magungunan kwari, in ji mista Rangaswa Muniappan, wani masani a cibiyar bincike ta IPM dake kasar Amurka. (Maman Ada)