in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar ta cimma yarjejeniyar hakar Uranium da kamfanin Areva na Faransa
2014-05-27 10:21:47 cri

Gwamnatin kasar Nijar da kamfanin Areva na kasar Faransa dake hakar karfen Uranium a kasar Nijar tun fiye da shekaru arba'in ta hanyar kamfanonin Somair, Cominak da kuma Imouraren a nan gaba, ma'adinan Uranium na yankin Arlit dake kuriyar arewacin jihar Agadez, sun cimma wata sabuwar yarjejeniyar harkar Uranium a ranar Litinin a birnin Yamai bayan an kwashe fiye da watanni biyar ana tattaunawa tsakanin bangarorin biyu, a cewar hukumomin kasar Nijar.

An rattaba hannu kan wannan yarjejeniya tsakanin ministan ma'adinai da cigaban masana'antun Nijar Omar Hamidou Tchana da babban darektan Areva, Luc Oursel.

Sabuwar yarjejeniyar da aka cimma za ta yi aiki bisa dokar ma'adinan kasar Nijar ta shekarar 2006, kuma kasar Nijar da Areva za su gabatar wa kwamitocin zartarwa na kamfanonin Somair da Cominak da manyan darektoci biyu 'yan asalin Nijar a shekarar 2014 da ta 2016 bi da bi.

Game da batun ma'adanan Uranium na Imouraren da za'a rika samar da ton 5000 a ko wace shekara, a cewar bangarorin biyu, fara aiki kansa na da nasaba da kyautatuwar kasuwar Uranium a duniya.

Haka kuma bisa wannan sabuwar yarjejeniya, kamfanin Areva zai zuba kusan Euro miliyan 90 wajen sake gina hanya tsakanin Tahoua da Agadez da kuma Arlit da aka fi sani da hanyar Uranium, kana wasu miliyan 17 za'a shigar da su wajen bunkasa ayyukan cigaba a yankunan arewacin Nijar dake kunshe ma'adinan Uranium. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China