in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana yajin aiki a Benghazi na kasar Libya
2014-04-07 16:21:32 cri
A jiya Lahadi 6 ga wata, aka fara yajin aiki a birnin Benghazi na kasar Libya, don nuna kin amincewa da matakai marasa amfani da gwamnatin wucin gadi da majalisar dokokin kasar suka dauka wajen warware matsalar tabarbarewar yanayin tsaron kasar.

Bisa labaran da aka samu daga kafofin watsa labaran kasar Libya, an ce, makarantu da dama a wurin sun dakatar da koyarwa, wasu kantuna su ma sun rufe shagunansu, sannan an rufe hanyar zuwa filin jirgin sama don haka an dakatar da fasinjoji da dama a filin jirgin sama domin rufe filin da yajin aiki ya haddasa, kuma wasu jiragen sama wadanda suke niyyar sauka a birnin Benghazi sun koma inda suka fito.

Yanayin tsaron kasar Libya na ci gaba da tada hankulan jama'ar kasa bayan yakin kasa, musamman ma a birnin Benghazi. Cikin shekara daya daya gabata, an sha fama da kisan gillar sojoji da kuma masu kiyaye tsaron yankin a birnin Benghazi, har ma an yi kashe tare da yin garkuwa da wasu fararen hula. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China