in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata Afrika ta kafa masana'antu domin samun cigaba
2013-03-26 16:02:17 cri

Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara ya bayyana a ranar Litinin a birnin Abidjan cewa, ya kamata Afrika ta daga matsayinta ta fuskar kafa masana'antu domin kasancewa shiyyar tattalin arziki mai tasowa.

Babban aikin cimma wannan buri shi ne gaggauta sauye-sauyen tattalin arzikinmu domin habaka kason ayyukan masana'antun kasashenmu da kuma nauyin fitar da kayayyakin da muka sarrafa zuwa kasuwannin duniya, in ji shugaba Alassane Ouattara a yayin bude taron shekara na hadin gwiwar ministocin kasuwanci da kudi na kungiyar tarayyar Afrika AU da kwamitin tattalin arziki na majalisar dunkin duniya kan Afrika ECA karo na 6.

Taron bisa jigon masana'antu a matsayin ginshikin samun cigaban Afrika kuma makasudin shi ne zurfafa hanyoyin kyautata masana'antu domin samun cigaban Afrika. A cewar shugaba Ouattara, ya kamata Afrika ta fuskanci kalubalen cigaban masana'antu ta hanyar daidaituwar siyasa, samar da yanayi mai kyau ga kananan masana'antu, kyautata yanayin takarar kasuwanci da kuma samar da gine-gine ta fuskar tattalin arziki dake muhimmanci wajen rage farashin sarrafa kayayyaki daidai gwargwado.

Taron Abidjan na gudanarwa jajibirin budewar taron kasashen BRICS dake kunshe da Brazil, Rasha, Indiya, Sin da Afrika ta Kudu a birnin Durban na kasar Afrika ta Kudu. Kuma Afrika za ta kansace matashiyar wannan taro na kwanaki biyu inda za'a mai da hankali kan kasashen BRICS da Afrika, huldar samun cigaba, dunkulewa da cigaban masana'antu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China