Hukumomi da kwararrun kasar Cote d'Ivoire sun bayyana niyyarsu domin cimma burin samar da issashen abinci ta fuskar noman shinkafa.
A yayin wata hirarsa tare da manema labarai a ranar Lahadi, babban darektan ma'aikatar bunkasa noman shinkafa ta kasa ONDR, Yacouba Dembele ya tabbatar da cewa, kasar ta kara rubanya kokarinta wajen cimma wannan muradin na samun cimaka nan da shekarar 2016. "Muna fatan samar da shinkafa tan miliyan 1,9 a shekarar 2016, bana yawan shinkafar da aka samar ya kai tan miliyan 1.3, a shekarar 2010 kuwa, tan dubu 700 ne." in ji mista Dembele.
Gwamnatin kasar Cote d'Ivoire ta kafa wani shirin kasa na bunkasa noman shinkafa bisa tsawon lakacin shekarar 2012 zuwa 2020, domin ganin tun daga shekarar 2016, an cimma dukkan bukatun al'ummar kasar wajen samun shinkafa mai inganci.
Shinkafa ta kasance cimaka ta farko da ake ci a kasar Cote d'Ivoire, ko wace shekara, kasar tana noma tan dubu 600 na shinkafa, amma bisa ga bukatun da aka kiyasta zuwa tan miliyan 1,5, lamarin dake tilasta wa kasar sai ta shigo da shinkafa daga waje. (Maman Ada)