Jam'iyyar FPI ta tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo ta nuna cewa, shirin sasanta 'yan kasar Cote d'Ivoire dake gudana cikin kasar wani ja da baya ne. Kwamitin tattaunawa bisa gaskiya da sasanta 'yan kasa na (CDVR) ya kasa kan aikin da aka dora masa, kuma shirin sasanta 'yan kasa wani abin koma baya ne, in ji jam'iyyar FPI a cikin wata sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi.
A cewar FPI, wannan kasawa na da nasaba da rashin niyyar siyasa ta gwamnatin kasar dake bayyana rashin sanya hannun shugaban kasar sosai a cikin wannan shiri na sasanta 'yan kasar Cote d'Ivoire baki daya. (Maman Ada)