A wannan rana, yayin da Zeidan ya halarci taron manema labaru gami da ministocin kasar, ya bayyana cewa, a ranar 10 ga wata, motoci kimanin 100 dauke da dakaru masu dauke da makamai sun yiwa otel da ya ke zaune kofar rago, kuma wadannan dakarun suka shiga cikin dakinsa,inda suka kwace wasu muhimman takardu da nau'rori masu amfani da wutar lantarki, da tufafi da sauransu. Ya ce, wadannan mutane suna aiki a hukumar juyin juya halin na Tripoli da ofishin yaki da aikata manyan laifuffuka, kuma akwai alaka da ke tsakaninsu da ma'aikatar kula da harkokin cikin gida, kuma akwai wasu mutanen da ke goyon bayan su, kuma wasu 'yan majalisar dokoki na wani bangaren siyasa na kasar sun taka muhimmiyar rawa a ciki. Sabo da haka, wannan lamari ba ma kawai batun awon gaba da mutane ba ne,amma wani makirci da aka kulla da nufin kifar da gwamnati mai ci.
Zeidan ya ce, yayin da ake tsare shi, dakarun da ke dauke da makamai sun yi masa tambayoyi game da dalilin sa na yin hadin gwiwa da Amurka don cafke dan kasar. Ya ce, Libya karamar kasa ce,akan Amurka,kuma ba zai yiwu ba, ya yi takara da kasar Amurka, a halin da ake ciki yanzu, ba zai iya yin kome ba, akan aika-aikar da Amurka ke aikatawa a kasar.(Bako)