A ranar 15 ga wata da yamma, jama'a kimanin dari biyar na birnin Tripoli sun yi zanga-zanga a yankin Garr Gul dake karkarar birnin don nuna adawa ga rikice-rikicen da dakaru 'yan kungiyar tsageru suka tada a birnin Tripoli. An kai hari ga masu zanga-zangar a wani sansanin kungiyar tsageru dake Misrata, inda aka harbi masu zanga-zangar ba zato ba tsamani da bindigogin ruwa da makaman roka. A sakamakon harin, ana ta samun rikice-rikice har zuwa ranar 16 ga wata, kana an tashi hankali ya fara kai wa sauran yankunan babban birnin kasar.
Firaministan gwamnatin wucin gadi ta kasar Libya Ali Zeidan ya yi wani jawabi a ranar 16 ga wata, inda ya bukaci dakaru 'yan kungiyar tsageru masu adawa da juna da su janye daga birnin Tripoli. Ya ce, ya yi kira ga dukkan dakarun da kada su shiga birnin Tripoli, domin wannan zai kawo mugun sakamako. (Zainab)