in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban mafarki na mai aikin sa kai, Li Jing
2014-04-01 15:19:16 cri

Jama'a masu sauraro, assalamu alaikum, barkan ku da wannan lokaci, barkan mu kuma da saduwa a cikin shirin mu na "in ba ku ba gida". Ni ce Jamila da zan jagorancin shirin a wannan lokaci. To, a cikin shirin mu na yau, za mu karanto muku wani bayani na musamman game da malama Li Jing, wata mai aikin sa kai a kasar Sin.

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, bisa kokarin da ake yi lokacin aiwatar da manufar raya yankin yammacin kasar Sin wadda take da makasudin bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma, tare kuma da kara karfafa harkokin tsaro a yankin, a kai a kai ne wasu lardunan da ke arewa maso yammacin kasar wadanda ba su samu yalwatuwar tattalin arziki yadda ya kamata ba, musamman ma jihar Xinjiang suke kara bukatar kwararrun da suke so su zo yankunan su yi aiki. A sa'i daya kuma, yanzu haka da kyar jama'a ke samu ayyukan yi a yankin da ke tsakiyar kasar, shi ya sa, daliban da suka kammala karatu a makarantun midil suka fi son su je jihar Xinjiang don cigaba da yin karatu a jami'a ko neman samun aikin yi a wurin. Malama Li Jing daya ce daga cikin su.

Malama Li Jing tana da shekarun haihuwa ashirin a duniya, kuma ta je Urumqi, babban birnin jihar Xinjiang ne daga birnin da ke gabar teku a gabashin kasar Sin. To, a lokacin da muka je domin hira da ita a wani safiya lokacin da ta farka daga barci ke nan ba da dadewa ba, hasken rana ya shigo daga taga, ya haska kan gadonta, Li Jing ta je ta wanke bakinta, kuma ta wanke fuska cikin 'dan lokaci, sannan ta fito waje inda muke, ta gaya mana cewa, "Yau da safe, ban farka daga barci cikin lokaci ba, saboda jiya da dare, na je jami'ar da nake karatu, na canza dakin da nake kwana a can zuwa wani daban, shi ya sa na dawo dakin da nake sauka a otel da tsakar dare wajen karfe biyu."

A farkon watan Satumban bara, wato na shekarar da ta gabata, an yi bikin baje kolin kasar Sin da Asiya da Turai wanda aka saba yin shi sau daya ko wace shekara a birnin Urumqi na jihar Xinjiang. A wancan lokaci, shugabannin gwamnatoci da 'yan kasuwa da suka zo daga kasashen duniya daban daban suka taru a birnin. Domin kara kyautata aikin karbar baki, hukumar da ta shirya bikin ta yi hayar dalibai masu aikin sa kai sama da 900 daga jami'o'in shida na jihar. Bayan jarrabawar da aka yi, Li Jing, wadda daliba ce a aji na hudu a jami'ar Xinjiang ta samu damar kasancewa mai aikin sa kai na bikin baje kolin. Ita dai tana karanta fannin ilmin gina hanyoyi da gadoji ne, aikinta na sa kai kuma shi ne karbar 'yan jarida wato manema labarai.

A wancan lokaci, dakin kwananta ya canja daga sashen arewa na jami'ar zuwa sashen kudu, shi ya sa Li Jing ta komo dakin da aka sauke ta a otel da sassafe. Ta ce, dukkan masu aikin sa kai suna zaune ne a otel saboda akwai ayyuka da yawa. A ko wane dare, Li Jing ta kan sadu da Motelif, mai kula da aikin farfaganda na birnin Urumqi, a wannan lokacin, su kan tattauna abubuwan da suka faru a wannan rana, kuma Motelif din kan ba ta sabon aiki. Li Jing ta ce, wani lokaci, su kan tattauna aiki yayin cin abinci, gaskiya ayyuka sun yi yawa, a don haka, ta kan yin saurin tafiya, har sauran abokan aikin nata ba su iya tafi tare da ita.

Li Jing ta fito ne daga Qinhuangdao, birnin dake gabar teku a gabashin kasar Sin. A shekarar 2009, ta tashi daga birnin zuwa Urumqi domin fara karatunta na fannin ilimin gina hanyoyi da gadoji a jami'ar Xinjiang.

Amma saboda an haife ta a garin da ke gabar teku, shi ya sa da kyar ta saba da yanayin Urumqi. Li Jing ta ce, tana kaunar teku, ta kan dauki hoto a bakin teku, kuma yanayin jihar Xinjiang busasshe ne, ya bambanta da na garin haihuwarta.

Li Jing ta yi mana bayani cewa, 'dan uwanta ya fara aiki ne a jihar Xinjiang a shekarar 2005 bisa bukatar da gwamnatin kasar Sin ta mika wa dalibai wato "A tafi yankin yammacin kasar inda aka fi bukatar mu", daga baya, 'dan uwanta ya aika mata wani babban hoto game da aikinsa a Xinjiang, a dalilin haka, Li Jing ta kara girmama 'dan uwanta da kuma sha'awa kan Xinjiang, don haka ta kuma tsai da kudurin zuwa jihar karatu. Ta ce, bayan da ta kammala karatu a jami'a, za ta shiga wata makaranta a birnin Changji na lardin domin koyar da dalibai. Ta ce, "Fannin karatuna ya fi dacewa da aiki a jihar Xinjiang, ina koyon ilmin gina hanya bisa yanayin kasa da muhalli na jihar, idan aka gina hanyoyin da ke hada wurare daban daban a Xinjiang, to tattalin arzikin jihar zai samu ci gaba yadda ya kamata, hakan ya sa na zabi Xinjiang don in yi aiki."

An ce, kullum iyaye na damuwar halin da yaransu ke ciki, musamman ma yayin da yaransu suka fita waje, ba su zaune tare da su, iyayen Li Jing su ma haka suke, su kan buga mata waya domin tambayar lafiyarta, amma Ji Jing ta kan sha aiki, har ba ta da lokacin yin hira da su, wani lokaci tana gaya musu cewa, su dan jira kadan, za ta bugo musu daga baya. Amma, kullum ba ta tunawa ta kira su cikin lokaci, saboda aiki ya kacirne mata a tsawon yini duk.

Wannan rana da karfe sha daya na safe, aka kammala taron manema labarai, daga baya sai wassu 'yan jarida suka tafi sansanin bikin baje koli domin yin tambayoyi ga baki wato intabiyu. Ko da suka isa wurin, sai Li Jing ta sanar da su cewa, za su hallara a nan da karfe biyu na rana domin komawa masauki wato otel, kuma ta tunatar da su cewar, kada su makara.

Kafin su tashi daga cibiyar bikin baje kolin, Li Jing ta yi yawo a wurare daban daban a ciki, domin ba da taimakon da ya kamata ga 'yan jarida, tana mai cewa, "Ko da yake ko wane mai aikin sa kai na da takamammen aikin shi, amma duk da haka, a ko da yaushe muna taimakawa juna saboda ayyuka sun yi yawan gaske, muddin dai aka bukace mu don ba da hidima, to za mu samar da taimako cikin lokaci."

Li Jing tana mai da hankali kan aiki sosai, alal misali, kafin ta kai 'yan jarida wurin aiki, kullum sai ta yi kidayar yawan mutane da za su shiga aikin da kuma lambobin wayarsu ta tafi da gidanka, idan wasu daga cikinsu ba su isa wurin haduwa cikin lokaci ba, za ta kira su ta waya, abin da kan sa har wasu su ji kunya saboda suna ganin cewa, sun bata mata lokaci.

Bayan da suka sauka a otel, kusan karfe uku ne da yamma, a cikin rabin awa kuwa, Li Jing za ta raka wasu 'yan jarida zuwa wani kamfani domin yin intabiyu, saboda ta dawo otel daga cibiyar bikin baje kolin ba da jimawa ba, babu lokacin cin abinci sosai, shi ya sa ta ci abinci kadan kawai, ta ce, wani lokacin ma ba ta ci kome, yunwa kan addabe ta, hakan ya sa ta kan adana alewa cikin jaka, in ta ji yunwa, sai ta jefa a baki ta tsotse.

Ya zuwa karfe takwas na dare, malama Li Jing ta sake komawa masauki wato otel daga kamfanin, sai dai me, lokacin hutu bai yi ba, domin lokacin taro ne, ta buga waya ga wasu masu aikin sa kai da ke cikin kungiyar karkashin jagorancinta, domin su je dakin Motelif yin taro. Yayin taron, za su yi wa juna bayanin aiki na wannan rana da kuma na kashegari. A daren wannan rana, za su tattauna aikin kai wasu 'yan jaridar da suka kammala aiki filin jirgin sama, ban da haka kuma, za su yi aikin shirya raka wasu 'yan jarida da za su je sauran wasu wurare domin cigaba da aikinsu. Ko da suka kammala dukkan ayyukansu, tsakar dare ya yi. Li Jing ta gaya mana cewa, sun saba da kwanciyar barci da karfe daya ko biyu tsakar dare, kuma su kan shiga barci cikin 'dan lokaci saboda gaskiya sun gaji sosai, kuma za su tashi daga barci da karfe bakwai na safe.

A ganin Motelif, mai kula da aikin farfaganda na birnin Urumqi na jihar Xinjiang, masu aikin sa kai suna kokarin aiki a ko wace rana, Motelif ya ce, a da, yana ganin cewa, dalibai da aka haife su bayan shekarar 1990 ba su iya aiki ba saboda wasa kadai suke so, amma sai ga shi a hankali ya fahimci cewa, lallai ashe suna cike da kuzari, kuma suna mai da hankali sosai kan aiki, har ma su kware ne a fannoni daban daban.

Bisa matsayinta na mai aikin sa kai, Li Jing ta gaya mana cewa, "Muna fatan za mu gudanar da aikinmu na sa kai yadda ya kamata kuma cikin nasara, saboda a gaban 'yan kasuwan kasashen waje da suka shiga bikin baje kolin, ba ma kawai muna wakiltar jihar Xinjiang ba, har ma muna wakiltar kasar Sin, shi ya sa dole ne mu yi iyakacin kokarinmu domin kammala aikin lami lafiya. In ba haka ba, jama'ar Xinjiang za su ji kunya, jama'ar kasar Sin za su ji kunya. Idan aka gamsu da aikinmu, to, za a bayyana cewa, masu aikin sa kai na kasar Sin na da himma, masu aikin sa kai na Xinjiang na da himma. Sannan mu ma za mu yi farin ciki kwarai."

Li Jing za ta shiga makarantar midil domin ba da ilmi ga dalibai bayan shekara daya wato bayan da ta kammala karatu a jami'ar. A game da wannan, Li Jing ta ce, tana fatan za ta ba da taimakonta ga cigaban Xinjiang. Ta ce, "Yanzu haka ni wata mai aikin sa kai ce, nan gaba zan kasance wata malama a makaranta, kamar yadda wata kila aka sani, bai kamata ba mai aikin sa ya nuna halin son kai, malamin koyar da ilmi a makaranta kuwa shi ma haka yake, bai kamata ba ya nuna halin son kai, shi ya sa, ina tabbatar da cewa, zan cigaba da nuna halin mai aikin sa kai yayin da nake aiki a makaranta, zan koyar wa dalibai dukkan ilmi kan gina hanya da nake da su, ta yadda za su yi amfani da ilmin yayin da suke aikin kyautata sufurin Xinjiang. Na taba gaya wa abokan karatuna cewa, ina da wani buri na gina Xinjiang, amma sun ce, akwai wuya na cimma burina, amma ina tsammani, ba haka ba ne, zan cimma wannan burin nawa. Muddin dai na ba da taimako ga gina kasa, ko karami ko babba, zan yi farin ciki."

Masu sauraro, yanzu haka a kasar Sin, kowa na tattauna "mafarkin kasar Sin", a hakika dai, mafarkin ko wanen basine na da alaka da bukatun bunkasuwar zaman al'umma a zamanin yanzu, Ana iya cewa, mafarkin kasar Sin mafarki ne na dukkan sinawa, kowanen al'umma a kasar Sin na sanya kokarinsu matuka domin ba da taimako ta hanyar kansu. Muddin dai aka yi kokari, to ko shakka babu, za a cimma burin.

Masu sauraro, karshen shirinmu na yau na "in ba ku ba gida" ke nan daga nan sashin Hausa na Rediyon kasar Sin, ku kasance lafiya. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China