140317-mata-a-harkokin-siyasa-lubabatu-danladi
|
Wani rahoto mai taken "mata a majalisa" da kungiyar tarayyar majalisun kasa da kasa ta fitar a ranar 4 ga wata a Geneva ya nuna cewa, a shekarar 2013, yawan mata 'yan majalisa a kasashen duniya ya karu da kashi 1.5% bisa na shekarar da ta gabata, wato ke nan, in an samu dorewar wannan ci gaba, mata za su tashi daya da maza a majalisun kasashen duniya nan da shekaru 20 masu zuwa. Rahoton ya kuma bayyana cewa, yawan mata a majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya wuce matsakaicin yawan mata a majalisun kasashen duniya.
Kungiyar ta tarayyar majalisun kasa da kasa ta fitar da wannan rahoto ne a dab da ranar da aka kebe wa matan duniya, wato ranar 8 ga watan Maris, kuma a daidai lokacin da ake gudanar da manyan taruka biyu a nan kasar Sin, wato taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da taron majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasar kasar, don haka, rahoton na da muhimmancin gaske.
Rahoton ya yi bincike kan yadda mata ke sa hannu cikin harkokin siyasa a kasashe 189 a duk fadin duniya, binciken da ya nuna cewa, matsakaicin yawan mata 'yan majalisa ya dau kashi 21.8% a majalisun kasa da kasa, wanda ya karu da kashi 1.5% bisa na shekarar 2012, karuwar da ta ninka ta shekarar 2011 har sau uku, lamarin da ya nuna cewa, yawan mata 'yan majalisa na karuwa cikin sauri. Mr.Anders B. Johnsson ya ce,
"Ana iya gano cewa, tun bayan zaben da aka yi a shekarar 2013, matsakacin yawan mata a majalisun kasa da kasa ya karu da kashi 1.5%, duk da cewa karuwar ba ta yi yawa ba, amma ta sa mata 'yan majalisa sun kai ga kashi 21.8% daga cikin baki dayan 'yan majalisa, kuma hakan ya faranta mana rai, in an kwatanta shi da kashi 20.3% na shekarar 2012. Ke nan in an ci gaba da samun karuwar, nan da shekaru 20 masu zuwa, mata za su tashi daya da maza a majalisun dokoki na kasa da kasa."
Abin lura shi ne, daga cikin kasashe 10 da ke kan gaba ta fannin yawan mata da ke cikin majalisunsu, akwai kasashe shida da suka kasance a nahiyar Amurka da Afirka, wadanda daga cikinsu, kasar Uganda ta fito a matsayi na farko, kasar da ke da mata 'yan majalisa da yawansu ya kai kashi 63.8%, daga ita sai kuma kasashen Andorra da Cuba da Sweden da Afirka ta kudu da Seychelles da Senegal da Finland.
To, sai kuma in aka dubi yawan mata 'yan majalisa a shiyyoyi daban daban, shiyyar nahiyar Amurka ta fi burgewa, inda kashi 25.2% na 'yan majalisa a kasashen shiyyar suka kasance mata. Ban da wannan, kasashen Larabawa sun kasance kasashen da suka fi saurin karuwar mata 'yan majalisa, inda a kasar Saudiyya a watan Janairu na shekarar 2013, akwai mata 30 da aka nada su a matsayin 'yan majalisar ba da shawarwari.
A ganin kungiyar tarayyar majalisun kasa da kasa, dalilai da dama ne suka yi sanadiyyar karuwar mata 'yan majalisa, kuma biyu daga cikinsu sun fi tasiri. Na farko shi ne dokar da aka kafa, na biyu kuwa shi ne wayewar kan al'umma. Mr.Anders B.Johnson, shugaban kungiyar tarayyar majalisun kasa da kasa ya ce,
"Na farko shi ne kafa doka, hakan ya iya samar wa mata damar shiga zabe da kuma cin zabe. Ana iya kebe wani kaso ga mata ta hanyar kafa doka, ko kuma wata jam'iyyar siyasa ta bayyana wani kason da ake bukata ga mata. In an lura, akasarin kasashen da 'yan majalisarsu mata ke karuwa suna da irin wannan doka." (Lubabatu)