in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar NFA na shirin gudanar da zaben shuwagabanninta
2014-03-24 15:16:09 cri

A Litinin din nan ne hukumar gudanarwar kwallon kafa a tarayyar Najeriya NFA, ta kaddamar da kwamitin shirya zabe, da kwamitin sauraron korafe-korafe, gabanin zaben shugabanninta dake tafe a karshen watan Agusta mai zuwa.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a jiya Lahadi, ta ce, kaddamar da wadannan kwamitoci, share fage ne na fara shirin zaben jagororin hukumar, wadda ke shan fashin baki wajen masharhanta harkokin wasanni.

An dai zabi mambobin wadannan kwmitoci biyu ne yayin babban taron hukumar, da ya gabata a birnin Warri na jihar Delta, a ranar 28 ga watan Nuwambar bara.

Yayin da zaben shuwagabannin NFA dake tafe cikin watan Agusta, zai ba da damar maye gurbin shuwagabannin hukumar masu ci, wadanda aka zaba tun cikin watan Agustan shekarar 2010, bisa zangon shekaru hurhudu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China