A gun taron manema labaru da aka yi a yau 22 ga wata da hukumar ikon mallakar ilmin fasaha ta kasar Sin ta shirya, an bayyana cewa, a cikin shekarar 2012 an samu ci gaba mai kyau a fannin ikon mallakar fasaha, inda yawan kayayyakin da aka kirkiro wadanda suka samu iznin mallaka a kasar Sin sun kai 217,105 wanda ya karu da kashi 26.1 cikin dari bisa na shekarar 2011.
Daga cikin wannan adadi, yawan kayayyaki da aka kirkiro cikin kasa ya kai 143,847 wanda ya karu da kashi 28 cikin dari bisa na shekarar 2011, kana ya kai kashi 66.3 cikin dari bisa na dukkan kayayyakin da aka kirkiro.
Ya zuwa karshen shekarar 2012, jimlar kayayyakin ta kai miliyan 1.111 a kasar Sin. (Amina)