Kafofin watsa labaru na kasashen waje sun ruwaito kididdigar da MDD ta yi a ran 12 ga wata cewa, yawan lambobin kere-kere da kasar Sin ta nemi samun iznin mallaka na musamman a shekarar 2011 ya karu da kashi 33.4 cikin dari, haka ya sa duk adadin nan da kasar Sin ta samu ya dauki matsayi na 3 a duniya.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayar da labari cewa, ko da yake akwai abubuwa da yawa dake kawo mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya, amma kamfannonin kasashe daban daban suna ci gaba da kirkiro sabbin kayayyaki, yawan lambobin kere-kere da ake neman samun iznin mallaka ya kai matsayin koli a tarihi, musamman ma a kasar Sin. Amma matsayi da kasar Amurka ta dauka a fannin lambar kira ya ragu zuwa na 6.
A game da haka, babban jami'in kungiyar ikon mallakar ilmin fasaha Francis Gurry ya ce, "A shekarar bara, kasashen Asiya sun fi kokarin neman samun lambobin kere-kere, kamar yadda kasashen Amurka da Turai suka yi a lokacin da, kana kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a kan wannan aiki."(Lami)