in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin Standard Chartered reshen Najeriya ya shirya liyafar kara dankon zumunci tare da kamfanonin kasar Sin
2014-03-06 20:28:24 cri

Taron da aka yi yau ya samu halartar manyan jami'an Sin da Najeriya, ciki har da babban manaja mai kula da harkokin kamfanoni na bankin Standard Chartered reshen Najeriya Mista Remi Oni, da babban jami'in kula da harkokin tattalin arziki da kasuwanci na ofishin jakadancin Sin dake Najeriya Mista Zhou Shanqing, da shugabar kungiyar hadin-gwiwar kamfanonin kasar Sin dake Najeriya Madam Jiang Pingping, gami da wakilai sama da 50 daga kamfanoni kasar Sin kusan 30.

A cikin jawabin da ya gabatar, Mista Remi Oni ya ce, alakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen Sin da Najeriya na dada inganta a 'yan shekarun nan, kuma ana kara samun kamfanonin kasar Sin wadanda suka je kasashen Afirka da ma Najeriya don zuba jari. Bankin Standard Chartered yana fatan karfafa hadin-gwiwa tare da kamfanonin kasar Sin a fannonin da suka shafi kasuwanci, hada-hadar kudi, samar da ababen more rayuwar jama'a da sauransu.

1 2 3 4
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China