Magatakardan MDD Ban Ki-Moon a ranar Litinin din nan, ya mika sakon taya murna ga shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma, mutanen kasar, har ma da cibiyoyin dake yankin Afirka ta yamma dangane da gabatar da zaben shugaban kasar da aka yi ran 17 ga watan Nuwamba cikin nasara da lumana a kasar ta Saliyo.
Sanarwar da ta fito ta hannun mai magana da yawun sakatare janar din na MDD ta bayyana cewar, wannan zaben da aka gabatar, ko shakka babu ya nuna dagewar jama'a na ganin demokradiyya ta zauna daram da kuma samun ci gaba a kasar.
Sakatare janar din ya jaddada muhimmancin ganin 'yan kasar ta Saliyo sun hada hannu don yin aiki tare a nan gaba, don haka, magatakardan MDD ya yaba alkawarin da shugaba Koroma ya dauka na hado kan daukacin 'yan kasar Saliyo don bunkasa sulhu a matakin kasa da kuma samun hadin kai.
Bisa sakamakon zaben da hukumar zabe ta kasar ta gabatar ranar Juma'a, Koroma ya sake samun nasarar hawa kujerar shugaban kasa karo na biyu, da yawan kuri'u kashi 58.7 daga cikin dari, sannan abokin hammayarsa Maada Bio na biye da shi da kuri'u kashi 37.4 daga cikin dari.A shekarar 2007 ne aka zabi shugaba Koroma a matsayin shugaban kasa.(Lami)