Bisa gayyatar da aka yi masa, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi ziyara a kasashen Nepal, Saudiyya, hadaddiyar daular Larabawa UAE, Qatar daga ran 14 zuwa 19 ga wata. Kuma ya halarci bikin kaddamar da taro na biyar na makamashin duniya da aka yi a Abu Dhabi babban birnin kasar hadaddiyar daular Larabawa. Ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi wanda ya rufawa Wen Jiabao baya, ya ce, ziyarar da Wen Jiabao ya yi a wannan karo ta kasance mataki mai kyau da shugaban kasar Sin ya dauka a fannin diplomasiyya a sabuwar shekara. Kuma, an samu ci gaba mai kyau cikin wannan ziyara.
Yayin ziyarar ta tsawon kwanaki shida, Wen Jiabao ya halarci ayyuka har 40, kuma ya yi jawabi a gun bikin kaddamar da taro na biyar na makamashin duniya da taro na hudu na 'yan kasuwa na dandalin tattaunawa kan hadin kai tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa kuma bikin kaddamar da taron zuba jari. Inda Wen Jiabao ya bayyana matsayin da Sin ta dauka wajen samun bunkasuwa mai dorewa tare da kiyaye muhalli, kuma ya bayyana tsare-tsare da manufofi da Sin ta dauka a wannan fanni. Kana ya ce, Sin na fatan kara hadin gwiwa da kasashen Larabawa da dai sauran kungiyoyin shiyya-shiyya da na duniya domin samun amincewa da juna ta fannin siyasa da kara hadin kai bisa manyan tsare-tsare.
Ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya nuna cewa, ana fuskantar mawuyacin yanayi a duniya, Sin da wasu kasashen kudancin nahiyar Asiya da wasu kasashen Gulf na kara sada zumunci tsakaninsu tare da habaka hadin gwiwa, ban da wannan kuma, Sin ta yi hadin kai da wadannan kasashe domin fuskantar sabon zarafi da yawan kalubale. A karkashin wannan hali, ziyarar da Wen Jiabao ya yi ta samu ci gaba mai kyau wajen samun amincewa da juna a fannin siyasa, kara yin mu'amala, zurfafa zumunci, habaka hadin gwiwa. Kuma ziyarar za ta samar da zarafi mai kyau wajen zurfafa dangantakar sada zumunci tsakanin kasar Sin da kasashen Gulf ta yadda za su samu bunkasuwa tare.(Amina)