A yayin taron manema labaran da aka gudanar bayan tattaunawar tsakanin Sergey Lavrov da ministocin harkokin wajen kasashen kwamitin hadin gwiwar kasashen Larabawa na yankin Gulf, Sergey Lavrov ya bayyana cewa, a halin yanzu, abin da ya fi muhimmanci wajen warware matsalar Syria ba wai kiran da aka yi wa shugaban kasar Bashar da ya yi murabus ba ne, muhimmin batu dai bai wuce tsayar da musayar wuta da kuma zubar da jini tsakanin bangarorin biyu na hamayya ba.
Kuma Sergey Lavrov ya soki lamarin kafuwar kungiyar tarayyar 'yan adawa, mai niyyar juyin juya halin kasar ta Syria a ran 11 ga wata a Doha, babban birnin kasar Qatar. Ya kuma mai cewa, kungiyar ba ta wakilcin dukkan kungiyoyin adawa na kasar Syria.
Amma a cikin sanarwar da aka bayar a wajen taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kwamitin hadin gwiwar kasashen Larabawa na yankin Gulf, an ce, kwamitin zai dauki karin matakai kan gwamnatin Syria, kuma zai yi kira ga MDD da ta kau da matsayin gwamnatin ta Syria da ke MDD.
A rana ta biyu ne bayan kafuwar kungiyar tarayyar 'yan adawa, mai niyyar juyin juya halin kasar ta Syria wato a ranar 12 ga wannan wata, sai kwamitin hadin gwiwar kasashen Larabawa na yankin Gulf ya amince da matsayinta na wakilin halal daya kadai dake wakiltar kasar Syria, kuma kwamitin ya nuna cewa, zai samar da wajababbun taimako da goyon baya ga kungiyar. (Maryam)