Wata sanarwar da kasar ta fitar a maraicen ranar Laraba 2 ga watan Oktoba ta ce, gwamnatin kasar ta Gambia ta janye daga cikin kungiyar ta Commonwealth, kana ta yanke shawarar cewa, ba za ta sake shiga kungiyar da ke da nasaba da wani na'u'i na mulkin mallaka ba.
Wannan matakin da kasar ta dauka ya zo ne kimanin shekaru 50 bayan da kasar ta Gambia ta shiga kungiyar ta Commonwealth a shekara 1965, ko da ya ke sanarwar ba ta yi wani karin bayani ba. (Ibrahim)