in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar UNICEF ta taimakawa yara masu fama da tamowa dubu 850 a yankin Sahel bana
2012-12-12 10:59:55 cri

Asusun tallafawa kananan yara na UNICEF na majalisar dunkin duniya ya fitar da wani rahoto a ranar Talata kan matsalar aikin jin kai a yankin Sahel, inda kungiyar ta bayyana cewa, ta rarraba taimakon abincin gaggawa zuwa ga kananan yara kimanin dubu 850 dake fama da rashin abinci mai gina jiki ko tamowa mai tsanani a shekarar 2012.

Wadannan alkaluma an ba da su ne bisa sakamakon binciken da aka samu a karshen watan Satumba, a yayin da adadin yaran dake samun jinya a lokacin yake da dubu 730.

A cikin watan Disamban shekarar 2011, kungiyar UNICEF ta yi hasashen cewa, yara miliyan 1.1 za su kasancewa cikin barazanar rashin abinci mai gina jiki. Amma tare da taimakon gaggawa na kungiyar tarayyar Turai, kasar Sweden, Danmark da Amurka, kungiyar ta samu damar rarraba nau'o'in abinci masu gina jiki da inganci.

Bisa kwarewarmu da ayyukan da muka gudanar a wannan shiyya, wannan ya darasin tunkarar wani babban kalubale domin kai taimako ga dukkan yaran dake wannan shiyya. An samu kaucewa wani bala'i. Ko da yake mun cimma nasara, amma duk da haka, ya kamata mu tsaya kullum cikin shiri domin har yanzu akwai yaran dake mutuwa bisa dalilan da za'a iyar kaucewa, in ji darektan wucin gadi na kungiyar UNICEF a wannan shiyya, mista Manuel Fontaine. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China