in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An zabi Sin da ta zama mambar hukumar kare hakkin 'dan adam ta MDD
2013-11-13 10:47:18 cri

An zabi kasar Sin da ta zama mambar hukumar kare hakkin 'dan adam ta MDD a ranar Talata bisa wa'adin shekaru uku. Sin dai na daga cikin kasashe 14, sabbin mambobin da aka zaba cikin mambobi 47 na hukumar a yayin babban taro karo na 68 na MDD.

Kasar ta Sin ta samu kuri'u 176 na amincewa daga kasashen mambobin MDD 192 da suka halarci taron a zagayen farko na zaben a ranar Talata da safe, lamarin da ya baiwa kasar hurumin wakilci na shekaru uku a hukumar da zai fara daga shekarar 2014 zuwa shekarar 2016.

Hedkwatar hukumar kare hakkin 'dan adam ta MDD tana birnin Geneva na kasar Swiss kuma shi ne wata babbar hukumar MDD dake aikin bunkasa da kare 'yancin bil'adama a duniya, a ranar 15 ga watan Maris din shekarar 2006, an kafa ta domin maye gurbin kwamitin kare 'yancin 'dan adam da aka kafa shekaru 60 da suka gabata.

An zabi kasar Sin a matsayin mambar kasashen da suka kafa hukumar a shekarar 2006 kuma aka sake zaben ta a wani sabon wa'adi na shekaru uku a shekarar 2009. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China