Shugaban kwamitin da ke nazari kan dalilin mutuwar Yasser Arafat, mista Tawfiq Tirawi ya bayyana a 'yan kwanakin baya cewa, gwamnatin Palesdinu ta riga ta karbi sakamakon rahoton likitocin Switzerland da Rasha, amma bai bada karin haske ba kan sakamakon da aka cimma.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Isra'ila, mista Yigal Palmor ya bayyana a kwanan baya cewa, kungiyar bincike ta kasar Switzerland ba ta taba neman takardar bayani daga asibitin Faransa ba, inda Yasser Arafat ya mutu, domin haka sakamakon ba zai kasance mai fa'ida ba. A cewarsa, kungiytar binciken Switzerland na bin umurnin wasu bangarori.
Game da ko Isra'ila ta kashe Yasser Arafat da guba ko a'a, Yigal Palmor ya ce Isra'ila bata kashe Arafat ba kuma kasarsa bata da hannu kan mutuwar Arafat.
Ya kara da cewa, mai yiyuwa ne mutuwar Arafat na da nasaba da rashin jituwa a tsakanin iyalan marigayin.(Danladi)