Wannan majiya ta gaya wa manema labaru cewa, Masu bincike wadanda suka zo daga kasashen Switzerland da Rasha sun gabatar da wannan rahoto ga hukumar Falesdinu. Amma ko da yake an kau da irin wannan yiyuwa, amma ba za a iya kawar da yiyuwa ta daban ba, wato mai yiyuwa ne Yasser Arafat ya mutu sakamakon wani sinadari mai guda na daban.
Sannan Tawfiq al-Tirrawi, shugaban kwamitin kula da aikin binciken dalilin mutuwar Yasser Arafat ya ki yin sharhi game da wannan rahoto, ya ce, gwamnatin Falesdinu za ta shirya wani taron manema labaru game da wannan sakamakon binciken gawar Yasser Arafat nan ba da dadewa ba. (Sanusi Chen)